16 Oktoba 2014 - 09:59
Ana Ci Gaba Da Allah Wadai Da Hukumcin Saudiyya Kan Sheikh Nimr

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna damuwarta ainun dangane da hukumcin kisan da wata kotun kasar Saudiyya ta yanke wa fitaccen malamin ‘yan Shi’a na kasar Ayatullah Sheikh Nimr Baqir al-Nimr tana mai cewa zartar da hukumcin na iya fusata al’ummar musulmi.

Yayin da yake magana kan wannan hukumcin, mataimakin ministan harkokin wajen na Iran kan lamuran kasashen Larabawa da na Afirka Husain Amir Abdullahiyan ya ce ko shakka babu wannan hukumcin zai sosa ran musulmin duniya sannan kuma zai fuskanci mayar da martanin al’ummomin duniya daban-daban.

 

Ita ma a nata bangaren kungiyar Amnesty International mai fafutukan kare hakkokin bil’adama ta bayyana tsananin damuwarta kan wannan hukumci inda ta bukaci gwamnatin Saudiyya da ta soke shi tana mai cewa hakan alama ce ta ci gaba da siyasar rufe bakin ‘yan adawa da gwamnatin Saudiyya ta jima tana aiwatarwa. Ita ma jam’iyyar Al-Wifaq ta kasar Bahrain ta ce babu wani abin da wannan hukumcin zai haifar face kara ruruta wutar adawa da gwamnatin Saudiyyan a cikin gida tana mai kiran da a soke hukumcin.

 

A kasar Saudiyyan ma dai rahotanni sun ce dubban mutanen garin Qatif ne suka fito kan tituna a daren jiya suna Allah wadai da gwamnatin ta Saudiyya da kuma jaddada goyon bayansu ga Sheikh al-Nimr din wanda a jiya kotun manyan laifuffuka ta Saudiyyan ta yanke wa hukumcin kisa saboda abin da ta kira samunsa da laifin rura wutar fitina da kuma bijirewa sarkin kasar. ABNA